fbpx
Connect with us

Hausa

Nasarorin Da Gwamna Emmanuel Udom Ya Samu A Mulkin sa

Published

on

Gwamna Emmanuel Udom

Gwamnan Jihar Akwa Ibom daya ne daga cikin fitattun ‘yan siyasa da suka cimma nasara a rayuwarsu ta siyasa da kuma shugabanci a dan kankanin lokacin da yayi a shugabancin dabya rike tun daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa yanzu a matsayin Gwamnan jihar Akwa Ibom.

Ya tsaya takarar Gwamna a watan Afrilun 2015 a karkashin tutar jam’iyyar PDP, sannan, an kuma zabensa a matsayin Gwamna Karo na biyu a jihar Akwa Ibom a shekarar 2019.

Yana daga cikin abinda yayi fice akansa shi ne, kokarin janyo mutane ayi tafiya tare da su wajen gudanar da Gwamnatin demokaradiyya domin hidimtawa al’umma. A komai nasa yana tuntubar mutane domin basu damar tafiya tare da ra’ayinsu a Gwamnati.

Gwamna Emmanuel a yunkurinsa na sake nauyi na shugabanci, ya sake rayar gundumar Eket tare da gina manya manyan hanyoyi wadan da suka kunshi masu hannu biyu da masu falle daya tare kuma da gyara da yawan asibitoci a jihar tasa.

A bangaren sha’anin tsaro kuwa, Gwamna Emmanuel ya tallafawa Hukumomin tsaro musamman cibiyar horas da ‘yansanda ta Awa Iman dake yankin karamar hukumar Onna, bugu da Kari, ya basu motocin sintiri masu sulke guda goma sha biyar tare da dukkan na’urorin sadarwa a tare da motocin.

Haka kuma, tun baya da ya sanya dokar ta baci a harkar ilimi, ya gina tare da inganta kusan dukkan makarantun hukuma dake jiharsa. A bangaren lafiya kuwa, ya gina asibitoci da inganta wadan da ake da su a jihar Akwa Ibom.

#

Trending